in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta hana shigo da kayayyaki daga Saudiyya
2016-01-08 10:19:35 cri
Rahotanni daga Iran na cewa, gwamnatin kasar Iran din ta bada umurnin hana shigo da dukkan kayayyaki daga kasar Saudiyya,tun bayan da dangantaka tsakanin Iran da Saudiyya ta tsananta sakamakon hukuncin kisa da ma'aikatar shari'a ta Saudiyya ta aiwatar kan wasu mutane 47 da take zarginsu da aikata ta'addanci, ciki har da malamin darikar Shi'a nan Nimr Al-Nimr.

Bayan yanke wannan hukunci wasu 'yan kasar Iran masu zanga-zanga suka kai hari tare da kona ofishin jakadancin Saudiyya dake kasar Iran. Don haka, a ranar uku ga wata ne gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da yanke dangantakar diplomasiyya da kasar kuma ta bukaci dukkan jami'an diplomasiyyar kasar Iran dasu fice daga kasarta cikin sa'o'i 48. Kana daga baya, kasar ta Saudiyya ta sanar da yanke dukkan huldar zirga-zirga da ciniki tare da Iran, sannan ta hana 'yan kasar ta zuwa kasar Iran. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China