Ma'aikatar harkokin wajen kasar Qatar, ta sanar da janye jakadanta daga kasar Iran a jiya Laraba, don nuna rashin jin dadin ta ga matakin da masu zanga-zanga 'yan kasar Iran suka dauka kan ofishin jakadancin Saudiyya dake Iran.
Ma'aikatar ta fidda sanarwar ne a daren jiya, ta kuma kirawo ofishin jakadancin Iran dake Qatar domin bayyana rashin jin dadin ta game da abun da ya faru.
Ban da wannan kuma, ita ma kasar Oman ta ba da sanarwar nuna rashin amincewa da aukuwar wancan lamari, tare da bayyana matakin da wadannan masu zanga-zanga suka dauka a matsayin abun da ya saba wa yarjejeniyar dangantakar diplomasiyya ta Vienna. Don haka Oman din ta ce ba za ta amince da hakan ba, kuma ya kamata ko wace kasa ta bi ka'idar hana tsoma baki cikin harkokin sauran kasashe, don tabbatar da zaman lafiya da lumana a wannan yanki. (Amina)