in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin hadin gwiwa da Saudiyya ke jagoranta sun musunta zargin da Iran tayi wai Saudiyya ta kai harin sama kan ofishin jakadancin Iran dake Yemen
2016-01-08 10:06:52 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Hossein Jaberi Ansari ya bayyana a jiya Alhamis cewa, Saudiyya ta kai hari ta sama kan ofishin jakadancin kasar Iran dake birnin Sana'a na kasar Yemen a daren ranar Laraba. Amma sojojin hadin gwiwa da Saudiyya ke jagoranta sun bayyana cewa, zargin kai harin da Iran ta yi ba gaskiya ba ne.

Kamfanin dillancin labaru na Iran ya sanar a jiya Alhamis cewa, harin da Saudiyya ta kai wa ofishin jakadancin Iran ya jikkata wasu masu aikin gadi tare da lalata ginin ofishin jakadancin. Ansari ya zargi Saudiyya da ta kai harin da kuma keta ka'idojin kasa da kasa na tabbatar da tsaron tawagogin jakadun diplomasiyya.

Sai dai biciken da aka yi, ya tabbatar da cewa, sojojin hadin gwiwar ba su dauki matakan soja kan ofishin jakadancin Iran dake Yemen da wuraren dake kewayensa ba, kana an tabbatar da cewa, ba a lalata ginin ofishin jakadancin Iran din ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China