Sashen ajiya na Amurka ya sanar da cewar, an sanya sunayen wasu 'yan kasar Iran su 6 da kamfanonin kasar 11 cikin jerin wadanda take tuhuma.
Sanarwar ta ce, wannan mataki ya yi daidai da shirin gwamnatin Amurkar na cigaba da farautar masu taimakawa Iran a shirinta na kera makamai masu linzami.
Adam Szubin, mai rike da sakataren kula da sashen ta'addanci da hada hadar kudade ta sirri, ya ce Amurka tana ci gaba da bayyana matsayinta a fili, cewar za ta karfafa takunkumin ta kan kasar Iran game da ayyukan da suka sabawa babban tsarin gudanarwa na JCPOA, wadanda suka hada da goyon bayan ayyukan ta'addanci da kasar ke yi, da daukar nauyin tashe tashen hankula a shiyyoyi, da cin zarafin bil adama, da kuma shirin makami mai linzami.
A yayin wani jawabi da ya gabatar a ranar Lahadin nan, shugaba Barack Obama na Amurka ya ce Amurkar za ta ci gaba da kakaba sabbin takunkumi kan kasar ta Iran muddin ta ci gaba da shirinta na mallakar makamai masu linzami.
Fadar white house ta ce, a ranar Asabar ne shugaban na Amurka ya rattaba hannu don amincewa da dage takunkumi kan kasar Iran dangane da shirinta na nukiliya, bayan hukumar sa ido kan kera makamai masu guba ta kasa da kasa IAEA ta ayyana cewar Iran ta mika wuya kan yarjejeniyar hukumar da aka cimma wato JCPOA.( Ahmad Fagam)