Yau Lahadi shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya bayyana fatansa na ganin kasashen duniya sun soke takunkumin da suka sanya wa kasarsa, tare da nuna imanin cewa, hakan zai bude wani sabon shafi ga ci gaban dangantaka a tsakanin Iran da gamayyar kasa da kasa.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na kasar Iran IRNA ya bayar, an ce, shugaba Rouhani ya furta cewa, Iran na rungumar duniya da hannu biyu biyu, tare da yin watsi da kiyayya da shakku da kuma makarkashiya.
Ban da haka, shugaba Rouhani ya yi tsokaci da cewa, cimma matsaya kan yarjejeniya kan batun nukiliya Iran daga dukkan fannoni ya kasance tamkar wata ishara ce ga ci gaban tattalin arzikin kasar. (Kande Gao)