in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya kawar da takunkumin da ya kakabawa bankuna biyu na Iran
2016-01-18 14:19:45 cri
A jiya ne kwamitin sulhu na MDD ya sanar da cewa, zai janye sunayen bankuna biyu na kasar Iran daga cikin jerin sunayen wadanda aka sanya musu takunkumi. A shekarar 2007 ne aka fara garkamawa wadannan bankuna biyu wato Bank Sepah da reshensa dake kasashen waje takunkumi

Sakataren janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Mista Yukiya Amano ya ba da sanarwa a ran 16 ga wata, inda ya ce,hukumarsa ta shaida cewa, Iran ta kammala ayyukanta na share fagen gudanarwar yarjejeniyar nukilya ta Iran da aka daddale, matakin da ya alamanta cewa, za a fara aiwatar da wannan yarjejeniya daga waccan rana, don haka kasashen duniya za su dage takunkumin da suka kakkabawa kasar Iran. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China