Yayin da shugaba Xi ke shirin fara ziyarar aiki a kasar Iran, "Jaridar Iran" ta kasar ta wallafa sharhin da ya rubuta mai taken "Shimfida wata makoma mai haske tsakanin Sin da Iran". A cikin wannan sharhi, Mista Xi ya ce, zai fara ziyararsa a kasar Iran bisa gayyatar da shugaba Hassan Rouhani ya yi masa, inda shugabannin kasashen biyu za su yi musayar ra'ayi kan wasu manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, matakin da ake fatan zai ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.
Yayin da shugaba Xi ya waiwayi tarihin mu'amala tsakanin kasashen biyu, ya ce, tun lokacin da kasashen suka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu a shekarar 1971, kasashen biyu na kokarin bunkasa dangantakar dake tsakaninsu duk da wasu kalubalolin da ake fuskanta. Ban da wannan kuma, shirin nan na "Zirin daya da hanya daya" da Sin ta gabatar ya sami karbuwa daga kasar Iran sosai, hadin gwiwar da kasashen biyu za su yi karkashin wannan shiri ya shafi bangarori uku, wato amincewa da juna ta fuskar siyasa, kawo moriyar juna, cudanya da juna da kara hadin gwiwa, yin mu'ammalar al'adu da kara bude kofa ga juna da yin hakuri da juna.
Daga karshe dai, shugaba Xi ya ce, duk da nisan da ke tsakanin kasashen biyu, kasar Sin tana fatan kara yin hadin gwiwa da Iran don samun bunkasuwa, da kuma habaka hadin kai da zurfafa zumunci, har ma da shimfida makoma mai haske tsakanin kasahen biyu. (Amina)