Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, a yayin tattaunawar sa da firaministan kasar Masar Sherif Ismail a birnin Alkahira, a ci gaba da ziyarar aiki da yake gudanarwa a kasar.
Ya ce ya ziyarci kasar ta Masar ne domin karfafa dankon zumunci tsakanin kasar da kuma Sin, da kuma fatan daga martabar dangantakar sassan biyu domin cimma sabbin nasarori.
Bisa wadannan dalilai a cewar shugaba Xi, ya kamata sassan biyu su rungumi tsarin ci gaba da bunkasar tattalin arzikin su, karkashin shirin "Ziri daya hanya daya", ta yadda hadin gwiwar su zai haifar da irin kyakkyawar nasarar da ake fata.
A nasa bangare firaminista Sherif Ismail, bayyana goyon bayan sa ya yi ga shirin "Ziri daya hanya daya", shirin da a cewarsa zai taka muhimmiyar rawa, wajen dunkule kafofin cinikayya da kasuwanci tsakanin Sin da kasashen Turai.