A daren jiya Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaran sa na kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi a birnin Alkahira.
Yayin ganawar ta su, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, a shekaru 60 da suka gabata, Sin da Masar sun girmama, da nuna goyon baya ga juna, sun kuma sada zumunta mai zurfi a tsakanin su. Ya ce Sin ta nuna goyon baya ga kasar Masar a kokarin tabbatar da zaman lafiya da raya tattalin arziki, da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a. Kaza lika kasar sa ta nuna goyon baya ga kasar Masar game da muhimmiyar rawar da take takawa a harkokin kasa da kasa, da yankuna, kuma Sin na fatan kokari tare da kasar Masar, wajen sa kaimi ga kafa tsarin kasa da kasa mai cike da adalci bisa tushen samun moriyar juna.
A nasa bangare, shugaba Al-Sisi ya bayyana cewa, a cikin shekaru 60 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin kasar sa da kasar Sin, an raya dangantakar sassan biyu yadda ya kamata. Kuma kasar Masar ta nuna yabo ga fasahohin bunkasuwa irin na kasar Sin, tare da fatan koyi daga wadannan fasahohi na Sin, da zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannoni daban daban, da kuma inganta dangantakar abokantaka a tsakaninsu a dukkan fannoni. (Zainab)