Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya OIC, a matsayin kungiya dake taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashen musulmin duniya, yana mai maraba da gudummawar kungiyar wajen fadada alakar kasar sa da daukacin kasashen musulmi.
Mr. Xi Jinping wanda ya yi wannan tsokaci yayin zantawar sa da babban sakataren kungiyar Iyad Ameen Madani, a ci gaban ziyarar aiki da ya kai kasar Saudiya a jiya Talata, ya kuma tattauna batutuwan da sassan biyu ke mai da hankali a kan su, da kuma harkokin musayar al'adu.
Ya ce, sassan biyu sun shafe sama da shekaru 40 suna musaya bisa sahihin kawance, sun kuma samar da gada dake hade mabanbantan al'adu da addinai da zamantakewa wuri guda.
Kaza lika shugaba Xi, ya jinjinawa matakin da kungiyar ta OIC ta dauka na yin Allah wadai da hare-haren ta'addanci da suka auku a kasar Sin, yana mai fatan fadada dankon zumunci, da hadin gwiwa mai ma'ana karkashin shirin "ziri daya da hanya daya" da daukacin kasashen musulmi.
Daga nan sai ya bayyana bukatar ci gaba da tattaunawa tsakanin kasashen na musulmi da sauran kasashen duniya, wajen warware matsalolin da al'ummar Falasdinawa ke fuskanta. Ya ce, Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa da kasashen musulmi, wajen warware dukkanin matsalolin shiyya-shiyya, da ma na kasa da kasa.
A nasa bangare, Mr. Iyad ya ce, OIC na girmama alakar ta da kasar Sin, kuma ta gamsu da matsayar Sin game da batutuwan Gabas ta Tsakiya. Har ila yau OIC na fatan Sin za ta taka rawar da ta dace, wajen warware kalubalen yankin, da ma na nahiyar Afirka.(Saminu)