A cikin sharhin, Mr. Xi ya ce bisa gayyatar da shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya yi masa, zai kai ziyara a kasar Masar. Kuma wannan ne karo na farko da ya kai ziyara a kasashen dake yankin gabas ta tsakiya da kasashen Larabawa, bayan da ya hau kujerar shugabancin kasar Sin. Kana shi ne karo na farko da ya kai ziyara a kasashen waje a shekarar 2016.
A cewar shugaban, kasar Masar ita ce kasa ta farko da ta kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninta da kasar Sin a cikin kasashen Larabawa, don haka dangantakar dake tsakanin sassan biyu ta zamo mafari na raya dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Larabawa, kana ta wakilci dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Larabawa.
Shugaban kasar Sin ya kara da cewa, fadin kasar Sin da kasashen Larabawa ya kai kashi daya cikin shida bisa jimillar fadin dukkan yankunan duniya, kuma yawan jama'arsu ya kai kashi daya cikin hudu bisa daukacin adadin mutanen duniya, kuma ko shakka babu akwai kyakkyawar makoma game da hadin gwiwar bangarorin 2.
Shugaban kasar Sin ya ce a nan gaba, bangarorin biyu za su ci gaba da raya hadin gwiwarsu a dukkan fannoni, da kuma dangantakar dake tsakaninsu, da sada zumunta, don amfanin jama'ar bangarorin biyu. (Zainab)