in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Saudiya suna hangen karin hadin gwiwwar masana'antu
2016-01-20 09:54:23 cri

Kasashen Sin da Saudiya sun amince da su daga matsayin dangantakar su zuwa wani matsayi na hadin gwiwwa a ranar Talatan nan, inda suke hangen karin hadin gwiwwar masana'antu.

Kasashen biyu sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar hadin gwiwwa ta fahimtar juna a hadin gwiwwar masana'antu bayan da sarkin Saudiya Salman bin Abdulaziz al-Saud ya tattauna da shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda ke ziyarar aiki a kasar.

Yarjejeniyar ya kuma ce, za su shiga cikin shirin 'ziri daya da hanya daya' na kasar Sin.

Shirin 'ziri daya da hanya daya' dake nufin hanyar siliki na tattalin arziki da hanyar ruwa na karni na 21 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya gabatar a shekara ta 2013 domin habaka ci gaban hadin gwiwwar kasashe da yankuna.

A lokacin ziyarar a Saudiya, shugabannin biyu sun amince da inganta dabarun sadarwa, su kuma daidaita tsarin shirin su na ci gaba, kafa dogon lokaci na hadin gwiwwa a fannin makamashi da kuma inganta tattaunawa tsakanin lokaci.

Shugaban kasar Sin dai ya fara isa kasar Saudiya ne a ranar Talatan nan a wata ziyarar aiki da zai kai kasashe 3 a yankin Gabas ta Tsakiya, a matsayin kasa ta biyu mafi girma a tattalin arziki dake neman hadin gwiwwar siyasa da tattalin arziki da yankin.

Shugaban kasar Sin, a lokacin ziyarar tashi a kasar Saudiya, ya samu kyautar yabo ta sarki Abdulaziz wanda sarki Salman ya ba shi, kyauta mafi girma a daraja a kasar.

Wannan ne dai karo na farko a cikin shekaru 7 da wani shugaban kasar Sin ya ziyarci kasar Saudiya. Shugaba Xi zai kuma ziyarci kasashen Masar da Iran a ziyarar shi ta farko zuwa kasashen waje a wannan shekarar tsakanin ranar 19 zuwa 23 na wannan watan.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China