Gabanin hakan, a kwanan baya, yayin da sakatare janar na kungiyar LAS Nabil el-Araby ke zantawa da wakilinmu, ya ce ziyarar shugaban kasar Sin a wannan karo tana da ma'anar musamman, kuma ta shaida irin cikakkiyar dangantakar dake wanzuwa tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa.
Araby ya ce, kasar Sin babbar kasa ce a duniya, kuma ta haifar da tasiri sosai game da samar da daidaito a duniya, kana tana goyon bayan moriyar kasashen Larabawa, da 'yancin kai na Falesdinu. Ya ce yayin ziyarar Shugaba Xi, bangarorin biyu za su tattauna don kyautata dangantakar dake tsakanin kungiyar da kasar Sin, da inganta hadin gwiwa a fannoni daban daban tsakaninsu, gami da daddale takardun fahimtar juna da dama.
Game da takardar farko da Sin ta fitar a fannin manufofin ta ga kasashen Larabawa, Araby ya ce wannan takarda ta nuna cewa, Sin tana da anniyar inganta hadin gwiwa da kasashen Larabawa, wanda hakan ya burge shi matuka. (Bako)