A jajibirin ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasar Masar, an kaddamar da littafin shi mai suna, "Xi Jinping: mulkin Sin" a Alkahira a ranar Talatar nan.
Littafin wanda aka wallafa shi a cikin harsuna da dama da suka hada da Sinanci, Turanci, Faransanci, Rashanci, Larabci, harsunan Spaniya, Portugal, da Jamus da Japananci ya shiga kasuwannin duniya bayan fitar shi.
A cinikin da aka yi a duniya baki daya, an sayar da kwafi miliyan 5.3, abin da ya samu zama na farko da wani shugaban kasar Sin ya rubuta da ya samu karbuwa haka tun daga shekara ta 1978 lokacin da aka bude kofa ga kasashen waje, aka kuma fara kwaskwarima a kasar.
Littafin ya kunshi jawaban shugaba Xi, hirar shi, da ganawar shi da manema labarai tsakanin watan Nuwamba na shekara ta 2012 zuwa Yuni na 2014.(Fatimah)