in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya fara zayarar aiki a Saudiya
2016-01-19 20:13:23 cri
A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Riyadh na kasar Saudiya, inda ya fara ziyarar aiki a hukunce a kasar.

A lokacin da ya isa kasar ta Saudiya shugaba Xi ya mika gaisuwa da fatan alheri ga al'ummomin kasar ta Saudiya, ya kuma bayyana cewa, kasar Saudi Arabiya babbar kasar musulunci ce, kana muhimmiyar mamba a kungiyar G20. Tun bayan da kasashen Sin da Saudiya suka kulla dangantakar diflomasiyyar a tsakaninsu yau shekaru 26 da suka gabata, ya zuwa yanzu, dangantakar dake tsakaninsu ta sami babban ci gaba, sun kuma karfafa fahimtar juna kan harkokin siyasa da kuma cimma sakamako da dama bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, lamarin da ya kawo babbar moriya ga al'ummomin kasashen biyu.

Kaza lika, a yayin ziyararsa a kasar Saudiya a wannan karo, shugaba Xi Jinping zai yi shawarwari tare da Sarki Salman bin Abdul-aziz Al Saud kan harkokin dake shafar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da wasu batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, domin ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Saudiya gaba.

Haka kuma, ana fatan cewa, za a sami sakamako masu gamsuwa da dama a lokacin ziyarar ta shugaba Xi a kasar Saudiya, sannan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Saudiya a fannoni daban daban za su hadaka, ta yadda za a kyautata hadin gwiwar dake tsakanin Sin da mambobin kasashen kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa dake yankin Gulf na GCC.

Bugu da kari, shugaba Xi Jinping zai kai ziyarar aiki a kasashen Masar da Iran bayan ya kammala ziyarar aikinsa a kasar Saudiya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China