in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da babban sakataren kungiyar GCC
2016-01-20 09:42:47 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da babban sakataren kungiyar hadin gwiwar kasashen Larabawa dake mashigin teku na Pasha (GCC) Abdul-Latif Al-Zayani a jiya Talata 19 ga wata.

A yayin ganawar ta su, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, kungiyar GCC kungiya ce dake taka muhimmiyar rawa wajen kula da harkoki masu alaka da mashigin tekun Pasha na yankin gabas ta tsakiya. A cikin shekaru 35 bayan da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da kungiyar GCC, an raya wannan dangantaka yadda ya kamata, kana akwai tushe mai inganci game da hadin gwiwarsu, kuma suna da kyakkyawar makoma wajen samun ci gaba.

Kaza lika shugaban na Sin ya yi fatan bangarorin biyu za su ci gaba da neman fannonin hadin gwiwa, da inganta dangantakarsu don sa kaimi ga amfanar jama'ar bangarorin biyu ta hanyar raya hadin gwiwa.

A nasa bangare, Al-Zayani ya bayyana cewa, kungiyar GCC tana da hulda mai kyau tsakaninta da kasar Sin. Kuma mambobin kungiyar sun amince da ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin bangarorin 2, da daga matsayin ta zuwa dangantakar abokantaka ta musamman, tare da kara yin imani da juna a fannin siyasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China