in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labaran Saudiya sun wallafa sharhin da shugaban Sin ya rubuta
2016-01-18 20:19:46 cri
A yau ne jaridar al Riyadh ta kasar Saudiya ta wallafa sharhin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta mai taken "bari mu zama abokan arziki da neman ci gaba cikin hadin gwiwa" gabanin ziyararsa a kasar ta Saudiya.

Shugaba Xi ya bayyana a cikin sharhin cewa, kasar Saudiya ta kasance kasa ta farko da zai kai ziyarar aiki a sabuwar shekara ta 2016, kana kasa ta farko cikin kasashen Larabawa da zai kai ziyarar aiki, tun bayan da ya hau kan ragamar mulkin kasar ta Sin.

Kuma, tun lokacin da aka kulla dangantakar diflomasiyya tsakanin Sin da Saudiya a shekarar 1990, dangantakar dake tsakaninsu ta kai wani sabon matsayi, musamman ma a shekarar 2008, bayan da kasashen biyu suka kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, dangantakar dake tsakaninsu ta bunkasa matuka, har ma hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu ta habaka bisa manyan fannoni ta hanyoyi daban daban.

Kaza lika, kasar Saudiya ta shafe shekaru da dama a matsayin babbar kasar dake samar da man fetur ga kasar Sin, kana babbar abokiyar cinikayya ta kasar Sin a yankin yammacin Asiya da kuma Afirka. Daga bisani kuma, kasar Sin ta kasance ta farko cikin manyan abokan cinikayyar kasar Saudi Arabiya a shekarar 2013, kuma wannan shi ne karo na farko da kasar Sin ta kai wannan matsayi.

Kasashen Sin da Saudiya suna da muhimmin tasiri a duniya, haka kuma, suna da kyakkyawar damar raya dangantakar diflomasiyya dake tsakaninsu a nan gaba, shugaba Xi na fatan shugabannin kasashen biyu za su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu domin ci gaba da kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen, ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu gaba bisa fannoni daban daban, ta yadda za a tallafawa al'ummomin kasashen biyu yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China