in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayyana ra'ayinta kan yadda Iran ta fara aiwatar da yarjejeniya batun nukiliyarta daga dukkan fannoni
2016-01-17 14:08:21 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya zanta da manema labarai na kamfanin dillancin labarai na Sin na Xinhua a yau Lahadi kan batun yadda kasar Iran ta fara aiwatar da yarjejeniya game da batun nukiliyarta daga dukkan fannoni, inda ya furta cewa, tun bayan da aka cimma daidaito kan wannan yarjejeniyar a watan Yuli na bara, kasashe shida da abin ya shafa da kuma Iran sun shirya sosai kan batun kaddamar da aiwatar da yarjejeniyar, hakan ya sheda niyyarsu da kuma alkawarinsu a fannin kiyaye yarjejeniyar. Don haka kasar Sin ta nuna musu yabo sosai kan batun.

Game da yadda za a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, Wang Yi ya bayyana ra'ayoyi uku na kasar Sin, wadanda suka hada da na farko, ya kamata bangarori daban daban su cika alkawarinsu ba tare da surutu da jan kafa ba a karkashin inuwar yarjejeniyar bisa ka'idojin zaman daidai wa daida, adalci, da kuma daidaito. Na biyu shi ne, ya kamata a kara amincewar juna. Batun nukiliyar Iran wani batu ne da ya shafi tsaron siyasa, wanda rashin amincewar juna ya kasance wani muhimmin bangare. Ya kamata bangarori daban daban su rika karfafa amincewar juna bisa hangen nesa, a kokarin aza harsashi mai inganci ga aikin ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar nan gaba. Na uku kuma shi ne, ya kamata a kiyaye hakuri da juna. Wannan yarjejeniya kan batun nukiliyar Iran wata yarjejeniya ce da aka cimma matsaya a kai bayan da aka yi rangwame da juna. Don haka ya kamata a ci gaba da kiyaye hakuri da juna, da neman ra'ayi daya tare da kasancewar bambanci, da warware sabani yadda ya kamata, a kokarin samun ci gaba bisa hadin kai. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China