Mr. Hong ya ce a yayin ziyarar, Mr. Zhang Ming ya yi musayar ra'ayoyi tare da bangarorin biyu, game da dangantakar dake tsakaninsu, kana ya yi kira gare su da kwantar da hankali.
Zhang Ming ya kai ziyara kasar Saudiyya ne a ranar 6 zuwa 8 ga watan nan, inda ya gana da mai jiran gadon sarautar kasar Mohammed bin Nayef, da ministan harkokin wajen kasar Adel al-Jubeir, da sauran manyan jami'an gwamnatin kasar.
Kaza lika Mr. Zhang ya ziyarci kasar Iran tsakanin ranekun 8 zuwa 10 ga wata, inda ya gana da ministan harkokin wajen kasar Mohammad Javad Zarif, ya kuma tattauna da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Ibrahim Rahimpour.
A yayin ziyarar tasa a kasashen biyu, Zhang Ming ya yi musayar ra'ayoyi tare da wakilan bangarorin biyu game da halin da ake ciki tsakanin su, musamman game da batun dangantakar su. Zhang Ming ya bayyana cewa, yana fatan bangarori daban daban da abin ya shafa da su kai zuciya nesa, tare da kara gudanar da shawarwari don sa kaimi ga sassauta halin da ake ciki.
Bangarorin Saudiyya da Iran sun yi bayani game da ra'ayoyinsu kan wannan batu, kuma sun nuna godiya ga kasar Sin, game da muhimmiyar rawa da take takawa a harkokin yankuna. (Zainab)