Bisa labarin da aka bayar, an ce, an kuma kai hari kan wani Otel na daban dake dab da Otel din Splendid, kuma rundunar tsaron kasar suna kan hanyar zuwa wannan wuri. Ban da wannan kuma, manyan asibitocin kasar dake birnin Ouagadougo hedkwatar kasar na baiwa mutane fiye da 40 jiyya.
Idan ba a manta ba, a daren jiya Juma'a 15 ga wata, wassu 'yan ta'adda sun mamaye wannan Otel tare da yin garkuwa da mutane da dama, ba da dadewa ba rundunar tsaro sun isa wuri tare da kewaye Otel da tankoki da motocin yaki, kuma sun yi musayar wuta da masu fafutuka. An ce, rundunonin soja na musamman na kasashen Faransa da Amurka sun shiga aikin ceto. (Amina)