in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardar MDD ya jinjina ma tarihin da aka kafa na rantsar da Shugaban kasar Burkina Faso
2015-12-30 09:51:37 cri
Magatakardar MDD Ban Ki-Moon a ranar talatan nan ya mika sakon taya murna ga Roch Marc Christain Kabore dangane da rantsar da shi a matsayin sabon Shugaban kasar Burkina Faso, wanda ya zama abin tarihi ma kasar.

Kabore dai an rantsar da shi a matsayin Shugaban kasar Burkina Faso a safiyar ranar talata wanda ya kawo karshen gwamnatin wucin gadi a kasar dake yammacin Afriika.

A sakon Mr. Ban Ki-Moon da ya mika ta hannun Karamin Sakataren majalissar Jeffrey Feltman a wajen bikin da aka yi a Ouagadougou babban birnin kasar, ya ce wannan ya zama wani lokaci cikin tarihin kasar. A don haka yake jinjina ma al'ummar kasar da shugabannin jam'iyyun siyasa saboda misali da suka nuna na gari wajen aiwatar da babban zaben lami lafiya a ranar 29 ga watan Nuwamba wanda cikin nasara ya kawo karshen gwamnatin wucin gadi.

Magatakardar Majalissar na dinkin duniya yace kamala babban zaben cikin lafiya da lumana a Burkina faso wani cigaba ne mai muhimmanci ba ma kawai ma kasar ba har ma yankin sahel baki daya, inda ake fuskantar kalubalen tattalin arziki da na zamantakewar al'umma, sannan takarar tsayawa kowane irin zabe na cigaba da zama wani tashin hankali, kuma a lokacin da kungiyoyin 'yan ta'adda, da safaran miyagun kwayoyi da ma gudun hijiran da ba shiri ke cigaba da barazana ga yanayin tsaron yankin.

Mr Ban ya kuma lura da cewa akwai manyan bukatu dake gaban sabuwar zarafin da jawo kowa a sulhunta a kuma cigaba da gina kasar tare a bangaren tsaro.

A dangane da hakan Magatakardar MDD ya ce majalissar a ko da yaushe za ta cigaba da goyon bayan kasar ta Burkina faso tare da bin hanyar zaman lafiya, gwamnatin demokradiya da kuma cigaban tattalin arzikin kasa. Har ila yau za ta cigaba da aiki da kungiyoyin yankin domin taimaka ma yankin na sahel a yammacin Afrika shawo kan ainihin dalilan rashin daidaito da zaman fargaba da take fuskanta.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China