Shugaba Kabore ya yi wannan kiran ne yayin bikin rantsar da shi a birnin Ougadougou, fadar mulkin kasar. Ya ce, kamata ya yi su dunkule kafofinsu na tsaro waje guda ta hanyar kafa wata dunlalliyar rundunar da za ta rika yaki da ayyukan ta'addanci.
Ya ce, Burkina Faso kamar sauran kasashen da ke yankin Sahel, ta shafe watanni da dama tana fama da barazanar ta'addanci.
Idan ba a manta ba a tsakiyar watan Disamba ne kasar Faransa ta gargadi 'yan kasarta da kada su ziyarci yankunan gabashin kasar ta Burkina Faso saboda barazanar ta'adancin da kasar take fuskanta.
Sannan kwanaki biyu gabanin zaben kasar na ranar 29 ga watan Nuwamba, wasu masu dauke da makamai sun kai hari kan wasu jerin gwanon motoci dauke da gwal da suka fito daga yankin arewacin kasar.
A kwanakin nan ne dai majalisar dokokin kasar ta Burkina Faso ta sanya hannu kan wata doka da za a iya yankewa duk wani mutum da aka same shi da hannu a aikata ta'addanci hukuncin daurin rai-da-rai ko zaman kaso na shekaru 10 zuwa 30
Bikin rantsar da shugaba Kaboren ya samu halartar shugabannin kasashen Cote d'Ivoire da Mali da Nijer da Senegal, da Benin da Togo, Gabon, da Ghana da kuma Guinea. (Ibrahim)