Sabon shugaban Burkina Faso ya yi alkawarin kawo alheri ga al'ummar kasarsa
Sabon shugaban kasar Burkina Faso, mista Roch Marc Christian Kabore ya yi alkawari a cikin jawabinsa na bikin shiga sabuwar shekara, na gudanar da shirin aikinsa na al'umma domin kyautata zaman rayuwar al'ummar kasa. A cewar shugaba Christian Kabore, wannan shekara ta 2016 ta fara tare da fatan alheri na ganin an cimma manyan sauye sauye, musammun ma a cikin rundunar sojojin kasar, gwamnati, hukumomin kasa, har ma da kafa wani kundin tsarin mulki na jamhuriya ta biyar domin zamanintar da hukumomin gwamnatin kasar baki daya. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku