A jiya Talata ne hukumar kula da kundin tsarin mulkin kasar Burkina –Faso ta ayyana Roch Christian Kabore a matsayin mutumin da ya lashe zaben shugaban kasar Burkina Faso da aka yi ranar 29 ga watan Nuwamban da ya gabata, bayan da ya samu kuri'u 1.669.214, kimanin kashi 53.46 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben, a yayin da babban abokin takararsa, Zephirin Diabre ya samu kuri'u 924.879, kimanin kashi 29.62 cikin 100.
Sakamakon wucin gadi da hukumar zabe mai zaman kanta (CENI), ta nuna cewa, mista Kabore ya samu kashi 53,49 na kuri'un da aka kada yayin da abokin hamayyarsa mista Zephirin Diabe ya samu kashi 29.65 na kuri'in da aka kada. (Maman Ada)