in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Burkina Faso ya bukaci da gudanar da bincike kan yadda aka tafiyar da rikon kwarya
2016-01-12 10:21:54 cri

Sabon shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore ya bukaci a ranar Litinin a birnin Ouagadougou, wani bincike kan yadda hukumomin rikon kwarya suka tafiyar da mulki, a tsawon watanni goma sha uku da suka biyo bayan hambarar da shugaba Blaise Compaore. Shugaban Burkina Faso ya bayyana fatansa na ganin, an gudanar da wannan bincike tun da wuri wuri, in ji Luc Marius Ibriga, shugaban babbar hukumar sanya ido kan aikin gwamnati da yaki da cin hanci (ASCE) a ranar Litinin.

Mista Ibriga dake magana bayan ganawa da shugaba Kabore, ya kara da cewa wannan bincike zai bayyana bambancin dake tsakanin aiki na gari da mugun aiki, kuma zai baiwa gwamnati ikon gudanar da siyarsa bisa sanin yadda ya kamata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China