Tsohon shugaban kasar Burkina Faso, Blaise Campare ya shiga tsaka mai wuya ganin cewa an bada takardar sammacinsa, game da batun kisan marigayi Thomas Sankara a shekarar 1987, a lokacin wani juyin mulkin da ya kawo shi mista Campaoren kan mulki. A cewar majiyoyin kotu, wannan takardar sammacin da ta shafi mista Campaore wanda yake kuma gudun hijira tun lokacin da aka kore shi daga mulki a karshen watan Oktoban shekarar 2014 a kasar Cote d'Ivoire, ta dauko asili tun a farkon watan disamban da ya gabata. (Maman Ada)