An sako Mutane da dama da aka yi garkuwa dasu bayan da jami'an tsaron kasar suka kaddamar da farmaki domin sake kwato otel din tare da ceto wadanda aka kame.
Kungiyar leken asiri na SITE wanda ke da sansani a kasar Amurka ta bayyana a shafinta cewa al-Qa'eda na yankin magreb AQIM ta dauki nauyin kai wannan harin a otel din Splendid na binin Ouagadugou ta hanyar hadewa tare da rundunar al-Murabitoon .
Otel din splendid wanda bai da nisa daga babban filin saukan jiragen saman birnin yana yawan samun baki daga kasashen yammcin da suka hada da ma'aikatan MDD da manema labarai, inji kafar yada labarai ta CNN.
Mutane uku dauke da manyan makamai da suka rufe fuskokin su sun isa otel din cikin motoci biyu inji wani da ya gane ma idanun shi. Haka kuma 'yan kasashen waje da yan kasar ma na cikin wadanda aka yi garkuwa da su inji ma'aikatar harkokin wajen kasar.
An yi ta jin tashin bindogogi da fashe fashen sinadari a harabar kasuwancin birnin da kusan karfe 7.30 na yammacin wannan rana, sannan an rufe otel din tare da kafa dokar hana fita har sai karfe 6 na safiyar asabar din nan.
Tun da farko dai wadansu mutane masu dauke da makamai kusan su 20 suka kai hari a kan jami'an tsaron dake sintiri a Tinakof da ke arewacin kasar kusa da kan iyaka da kasar Mali inda suka hallaka mutane biyu da suka hada da dan sanda da farar hula daya.