in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burkina Faso: An baiwa diyya ga mutane fiye da 900 da suka jikkata a yayin bore da yunkurin juyin mulki
2015-12-17 10:46:34 cri
'Yan kasar Burkina Faso da suka ji rauni a yayin zanga zangar 'yan kasa da ta kori tsohon shugaban kasar Blaise Compaore daga mulki a cikin watan Oktoban shekarar 2014 da kuma a yayin yunkurin juyin mulki na ranar 16 ga watan Satumba, suka samu diyya, a cewar wasu majiyoyi masu toshe a ranar Laraba. Wadannan mutane ko wane daga cikinsu ya samu tallafin kudi na Sefa jika dari uku kwatankwacin dalar Amurka dari biyar, kwanaki hudu bayan gwamnatin wucin gadi ta ba su lambar yabo, a cewar wadannan majiyoyi. A jimilce, an yi rajistan mutane 652 da suka jikkata a lokacin boren al'ummar kasar a karshen watan Oktoban shekarar 2014, kana mutane 217 a yayin junkurin juyin mulki na hannun daman Compaore, Janar Gilbert Diendere. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China