Burkina Faso: Zababben shugaba zai kama aiki kafin shekarar 2016
Shugaban wucin gadin kasar Burkina Faso, Michel Kafando, ya furta a ranar Laraba cewa zababben shugaba Roch Marc Christian Kabore zai iya kama aiki kafin karshen shekarar da muke ciki. Da yake amsa wata tambaya dake da nasaba da bikin rantsar da zababben shugaba, bayan wata ganawar da ya yi tare da wannan sabon shugaba, mista Kafando ya bayyana cewa wannan zai kasancewa abu na farko cikin tarihin Burkina Faso, wani shugaban farar hula zai mika mulki ga wani shugaban farar hula. Mista Kabore da aka zabe shi tun a zagayen farko na zaben shugaban kasa da kusan kashi 54 cikin 100, ya nuna yabo ga goyon baya da kulawar hukumomin wucin gadi wajen shirya zabuka na watan Nuwamban shekarar 2015. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku