Wadannan jam'iyyun siyasa daga cikinsu akwai kawancen jam'iyyar UNIR/PS na mista Benewende Sankara, wani babban mai adawa da tsohon shugaban kasa Blaise Compaore a tsawon tarihi. An kafa wannan gungun 'yan majalisa dake kuma cikin kawancen jam'iyyu maso rinjaye dake goyon bayan shugaban kasa domin kare maradun kasar da kuma amsa bukatun al'ummar kasar a bangarori daban daban, cewar kakakinsa. (Maman Ada)