Burkina Faso na shirya takardun neman tuso keyar tsohon shugaban kasar Blaise Compaore
Hukumomin kasar Burkina Faso sun fara hada takardun neman tuso keyar tsohon shugaban kasar Blaise Compaore, da yanzu haka kotun kasa da kasa ta bada sammacinsa game da kisan Thomas Sankara a shekarar 1987. Takardar neman tuso keyarsa za a mika ta bada jimawa ba ga Cote d'Ivoire, kasar da ta ba tsohon shugaba Compaore mafaka, wanda kuma tun a farkon watan Disamba aka bada sammacinsa. Haka kuma, baya ga tsohon shugaban Burkina Faso da aka kora a karshen watan Oktoban shekarar 2014, Hyacinthe Kafando mataimakin ofisa na rundunar dake tsaron fadar shugaban kasa, kotu na nemansa tun daga ranar 27 ga watan Agustan shekarar 2015. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku