Babban magatakardan MDD Ban Ki Moon ya gabatarwa babban taron majalisar wani shiri a ranar jumma'an nan 15 ga wata dake da jigon "magance tsattsauran ra'ayi", inda ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki mataki bai daya don yin rigakafi da kuma yaki da ayyukan nuna karfi tuwo da masu tsatsauran ra'ayi suke aiwatarwa, haka kuma, ya ba da shawarar kafa irin wannan shirin matakai a kasashe da yankuna daban-daban.
Yayin da Mista Ban ya ke bayyani kan wannan shiri a gun babban taron majalisar, ya ce, tsattsauran ra'ayi ya zama tamkar barazana ne ga tsarin dokokin MDD, wanda kuma ke kawo babbar illa ga zaman lafiyar kasa da kasa da na shiyya-shiyya, danyen ayyukan da IS da Boko Haram da dai sauransu suka yi babu imani a ciki, kuma ba za a amince da shi ba.
Mista Ban ya kara da cewa, tsattsauran ra'ayi ba wai wani addini, wata kasa ko wata al'umma yake shafa ba, shi ya sa tinkarar wannan kalubale wani muhimmin aiki ne na majalisar. Shiri ya gabatar da hakikkanin shawarwari fiye da 70 ga kasashe daban-daban dangane da tinkarar matsalar. (Amina)