Tuni bangarorin da abin ya shafa suka amince da daukar matakan soji ga kungiyar Taliban, kasar Afghanistan tana fatar shawarwari na wannan zagaye, da irin matakan da aka dauka za su dakile aniyar kungiyar Taliban wajen daina kai hare hare a lokacin bazara.
Sai dai har zuwa yanzu, kungiyar Taliban ba ta mayar da martani game da taron shawarwarin ba. A baya dai manyan jami'an kungiyar sun taba bayyana cewa, ba sa nuna adawa ga yunkurin siyasa, amma ba su yanke shawarar shiga shawarwarin da gwamnatin Afghanistan ba.
A ranar 11 ga wannan wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin, Hong Lei, ya ce, kasar Sin tana goyon baya ga yunkurin sulhuntawa na Afghanistan da ke karkashin shugabancin al'ummarsu, kuma tana fatan yin kokari tare da bangarorin da abun ya shafa, don samar da taimako da gudummawa ga kasar, bisa tushen girmama mulkin kai gami da la'akari da anniyar bangarorin da abun ya shafa.(Bako)