in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na goyon bayan MDD wajen daukan matakin da ya dace a kan matsalar makaman nukiliyar kasar Korea ta arewa
2016-01-15 20:01:40 cri
A yayin da yake ganawa da manema labarai tare da takwaransa na kasar Switzerland Didier Burkhalter a nan birnin Beijing a Juma'an 15 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa,. Sin na nuna goyon baya ga kwamitin sulhu na MDD da ya dauki matakin da ya dace don warware matsalar nukiliya ta kasar Koriya ta arewa wadda ta jawo hankali kasashe daban-daban.

Mista Wang ya ce, gwajin nukiliyar da kasar ta Korea ta arewa ta yi a wannan karo ya sabawa kudurorin MDD da abin ya shafa, kuma ya sabawa muradin kawar da makaman nukiliya a zirin Korea, don haka Sin ta goyi bayan kwamitin da ya dauki matakin da ya dace.

Ya ce a ganin kasar Sin, ya kamata an kiyaye dokokin MDD, da tsarin hana yaduwar makaman nukiliya, a matsayin kasar dake da kujerar dindindin a kwamitin sulhun, Sin za ta yi iyakacin kokarin tuntuba da sulhuntawa tsakanin bangarori daban-daban. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China