Rahoton ya ce, sakamakon faduwar farashin muhimman kayayyaki da raguwar cinikayya da jari, da ma tangal-tangal da ake samu game da hada-hadar kudi, a shekarar 2015, yawan karuwar tattalin arziki da aka samu a shekarar 2015 ya yi kasa da yadda aka yi hasashe. Nan gaba, saurin bunkasuwar tattalin arziki na duniya zai dogara ne ga farfado da tattalin arziki a manyan kasashe, da tabbatar da farashin muhimman kayayyaki, da canja salon raya tattalin arziki da sayayya da kasar Sin ke yi. Duk da cewa, muhimman kasashe masu saurin bunkasuwar tattalin arziki ba su samu saurin karuwar tattalin arziki ba, amma bisa saurin farfadowar tattalin arzikin kasashe masu wadata, a bana, yawan bunkasuwar tattalin arzikin duniya zai kai kashi 2.9 cikin 100.(Bako)