Kafofin watsa labaru na kasar Italiya sun ba da labari jiya Litinin cewa, ma'aikatan ceto sun yi nasarar ceto 'yan gudun hijira 35 a gabar tekun dake kusa da birnin Puglia a kudancin Italiya, amma duk da haka, wata mace ta rasa ranta.
Binciken da aka gudanar ya gano cewar, 'yan gudun hijira sun fito ne daga kasar Somaliya, kuma yawansu ya kai mutane 40, baya ga macen da ta rasu, har yanzu akwai mutane 3 ko 4 da suka bace. Wasu 'yan gudun hijira sun bayyana cewa, masu satar mutane ne suka tura wasu mata cikin teku.
Bisa kididdigar da kungiyar kula da 'yan gudun hijara ta duniya ta fitar, ya nuna cewar, yawan bakin haure da suka kaura zuwa nahiyar Turai ta hanyar tekun Bahar Rum a shekarar bara, ya kai fiye da miliyan daya, kuma mutane 3700 daga cikinsu sun mutu ne a lokacin da suke kokarin ratsa tekun Bahar Rum.(Lami)