in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta fidda sabbin matakan yaki da masu tsattsauran ra'ayi
2016-01-09 13:39:25 cri
A ranar jumma'an nan 8 ga wata, gwamnatin kasar Amurka ta fidda wasu sabbin matakai domin fuskantar da karin kalubalolin da 'yan ta'adda suka haifar wa kasa da kasa a halin yanzu. Kana matakan da ta dauka sun hada da kafa wata tawagar musamman da kuma wata cibiyar tuntubar bangarorin kasa da kasa da abin ya shafa, domin yin kira ga bangarorin kasar Amurka da na kasa da kasa da su aiwatar da ayyukan yaki da ta'adanci cikin himma da kwazo.

Kaza lika, kakakin kwamitin tsaron kasa na fadar White House ta Amurka Ned Price ya fidda wata sanarwa cewa, harin ta'addanci da aka kai a birnin Paris na kasar Faransa a karshen shekarar da ta wuce, da kuma harin bindigogin da aka kai a birnin San Bernardino na jihar California ta Amurka sun nuna mana cewa, ya kamata kasar Amurka, gamayyar kasa da kasa da hukumomi masu zaman kansu su dauki matakai yadda ya kamata domin hana shigar da karin mutane cikin kungiyar IS da dai sauran kungiyoyin ta'addanci. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China