Wannan dokar da aka zartas da ita a ranar 27 ga watan Disamban bara, ta yi tanadi kan yadda za a tabbatar da kasancewar wata kungiya da membobinta a matsayi na ta'addanci, da yin rigakafi da aikin ta'addanci, da yadda za a gudanar da ayyukan leken asirrin da suka shafi ayyukan ta'addanci, da ma yadda za a gudanar da bincike da tinkarar harin ta'addanci, da yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a wannan fanni da sauransu.
Tashar yanar gizo ta internet ta ma'aikatar harkokin waje ta Rasha ta ba da bayanin sharhi cewa, wannan ne muhimmin matakin da Sin ta dauka a fannin doka wajen yaki da kowane irin ta'addanci, wanda zai taimaka ga hadin gwiwa tsakanin Rasha da Sin a wannan fanni.
Ban da haka, a nasa bangare, wani masanin Kenya kan batun tsaro ya furta cewa, ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi, babban kalubale ne da bil'adam ke fuskanta, wadanda suka kawo babbar barazana ga zaman lafiya a duniya. Zartas da dokar yaki da ta'addanci da gwamnatin Sin ta yi, ya bayyana kwarin gwiwarta na yaki da ta'addanci.(Fatima)