in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashe daban-daban sun ba da jawabin murnar sabuwar shekara
2016-01-01 17:35:05 cri

Shugabannin kasashe daban-daban sun ba da jawabin murnar sabuwar shekara, inda suka yi fatan samun kwanciyar hankali da wadata a kasashen su, sannan kuma da fatan kasancewar wata duniya mafi zaman lafiya da karko.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce, kasar ta taya murnar cika shekaru 70 da samun nasarar yakin tsaron kasar a shekarar 2015, kaka da kakanin Rasha sun gabatarwa jama'ar kasar abin koyi na tinkarar mawuyacin hali cikin hadin gwiwa, matakin da zai amfana wajen taimakawa 'yan kasar Rasha da su tinkarar kalubaloli irin daban-daban da ake fuskanta yanzu.

Shi ma, a nasa bangare, shugaban kasar Faransa François Hollande ya ce, ko da yake kasar tayi fama da hare-haren da 'yan ta'adda suka kai a shekarar 2015, amma ba ta mika wuyanta ba ko kadan. Duk da cewa kasar na fuskantar barazana mai tsanani, amma rundunar kasar sun cimma wasu nasarori ta fannin dakile IS. A nan sai shi ya yi kira ga 'yan Faransa da su goyi bayan shirin gyara kundin tsarin mulkin kasar wanda zai hana duk wani dan ta'adda ya zama dan kasar.

Shi ma shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya ce, kasar sa ta yi iyakacin kokarinta don yaki da kungiyar Boko Haram a shekarar bara, shi ya sa ya nuna godiya da mutuntawa ga runduna da jama'a da suka shiga wannan aiki, kuma ya nuna godiya ga kasashe da suka baiwa kasarsa taimako da goyon baya wajen yaki da kungiyar ta Boko Haram. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China