Ban Ki-Moon wanda ya fidda sanarwar hedkwatar M.D.D. dake birnin New York, ya kara da cewa abun da gwamnatin Koriya ta Arewan ta yi ya haifar da babbar damuwa ga kasashen duniya, duk da cewa sau tari, kasashen duniya su sha kira gare ta da ta dakatar da wadannan ayyuka, amma hakan bai hana ta gwajin nukiliyar sau da dama ba.
Mr. Ban ya ce hakan ya keta kudurori da dama na kwamitin sulhun M.D.D.. Kuma matakan da kasar ta dauka sun lahanta tsaro a wannan yanki, tare da dakile kokarin da kasashen duniya ke yi na hana yaduwar makaman nukiliya a duniya. Ya kuma bukaci Koriya ta Arewa da ta daina wadannan ayyuka nan take.
A wannan rana, kwamitin sulhu na M.D.D. ya ba da wata sanarwa ta kafofin watsa labaru, wadda ke Allah wadai da gwajin nukiliyar Koriya ta Arewan. A cikin sanarwar, an ce, mambobin kwamitin sulhun M.D.D. sun yi taron gaggawa, inda aka tattauna tsanantar halin da gwajin nukiliyar ya haifar.
Wannan gwaji dai ya keta kuduri mai lamba 1718 da na 1874 da na 2087, da na 2094, ya kuma kawo kalubale ga tsarin hana yaduwar nukiliya a duniya, tare da haddasa matsaloli ga aikin samar da zaman lafiya da tsaro a kasashen duniya. Mambobin kwamitin sulhun M.D.Dr. sun ce za a zage damtse don tsara daftarin shirin yaki da wannan mataki na Koriya ta Arewa.
A wani ci gaban kuma, fadar White House ta Amurka ta ce, bisa kwarya-kwaryan sakamakon bincike da Amurkan ta gudanar game da gwajin nukiliyar da Koriya ta Arewa ta yi a wannan rana, an gano cewa sakamakon bai dace da furucin harbar makamin kare dangi ba, kamar yadda Koriya ta Arewan ta sanar.
Kakakin fadar White House Mogens Lykketoft ya ce, Amurka tana ganin cewa, gwajin nukiliya da Koriya ta Arewa ta yi ya zamo tsokana ga kasashen duniya, kuma ya keta kudurorin kwamitin sulhu na M.D.D. Kana idan kasar ta ci gaba da daukar irin wadannan matakai, hakan zai jawo a mayar da ita saniyar ware. (Bako)