Wata majiya ta sheda a ranar Lahadin nan cewar, an kaddamar da harin ta'addanci kan karamin ofishin jakadancin kasar Indiya dake birnin Mazar-i-Sharif dake arewacin kasar Afghanistan. Amma, an ce, ma'aikatan karamin ofishin ba su rasa rayuka ko ji rauni ba.
Sai dai majiyar ta ce, biyu daga cikin maharani hudu sun kwanta dama, bayan da dakaru na musamman na Afghanistan suka yi musu barin wuta.
Wannan hari dai ya zo ne kwana guda bayan wani harin da aka kaddamar kan sansanin sojojin kasar Indiya a garin Pathankot dake arewacin yankin Punjab. Jami'an tsaron kasar Indiya 7 suka rasa rayuka a sakamakon harin, yayin da aka fatattake biyar daga cikin maharani shida.
Ana ci gaba da samun hare hare ne a a daidai lokacin da kasashen Indiya da Pakistan suke shirin gudanar da tattaunawar ministocin harkokin waje a birnin Islamabad nan da makonni biyu masu zuwa.(Ahmad Fagam)