Sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ba da wata sanarwa, inda ya yi Allah wadai da matakin Koriya ta Arewa na ci gaba da kera makaman nukiliya da na kare dangi, ya kuma bukaci Koriya ta Arewa da ta martaba ka'idojin kasa da kasa kana ta hanzarta kawo karshen shirinta na kera nukiliya da makaman kare dangi kwata-kwata, don shiga cikin shawarwarin kawar da makaman nukiliya a duniya.
Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa,shirin makaman nukiliya na Koriya ta Arewa, da gwaje-gwajen makaman nukiliya da ta yi a zirin Koriya wata babbar barzana ce ga zaman lafiya da tsaro, kana babban koma baya ne ga shirin hana yaduwar makaman nukiliya a duniya.
A ranar 6 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa ya ba da wata sanarwa cewa, Faransa ta yi kakkausar suka game da gwajin makaman nukiliya da Koriya ta Arewa ta gudanar.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Belarus Dmitry Mironchik ya ce, Belarus ta yi kira ga kasar Koriya ta Arewa da ta martaba kudurin kwamitin sulhu na M.D.D. na kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya ba tare da gindaya wani sharadi ba, sannan ta daina aika abubuwan da za su dagula al'amura a zirin na Koriya.(Bako)