Bisa labarin da aka bayar, an ce, wani kakakin kungiyar Al shabaab ya ce, kungiyar ta dauki alhakin kai wannan harin a wannan sansanin dake kan iyakar da ke tsakanin Somaliya da Kenya, wadda ke kunshe da sojojin daga kasar Kenya.
An ba da labarin cewa, sojojin sansanin suna ci gaba da yin musayar wuta da 'yan kungiyar, abinda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama. (Amina)