Kwamitin sulhu na MDD ya ba da wata sanarwa a ran 1 ga wata, don yin Allah wadai da harin da kungiyar Al Shabaab ta kaiwa wani Otel dake birnin Mogadishu na kasar Somaliya.
Sanarwar ta ce, kwamitin ya jajantawa iyalan mamatan, tare da nuna kyakkaywan fatan samun sauki cikin sauri ga wadanda suka jikkata. Mambobin kwamitin sulhu na MDD za su ci gaba da nuna goyon baya wajen tabbatar da zaman lafiya da karko a Somaliya, ko wane irin matakin ta'addanci ba zai iya kawo tasiri ga wannan niyyar tasu ba.
Haka kuma, mambobin kwamitin sun nanata cewa, kowa ne irin matakin ta'addanci na kasancewa wata babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya baki daya, dalilin haka ba za a amince da shi ba ko kadan.
Kungiyar Al Shabaab ta kai harin kunar bakin wake a ran 1 ga wata a wani Otel din dake birnin Mogadishu na Somaliya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 12. (Amina)