Kakakin yankin na lower Shabelle Mohamed Hussein Shino ne ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewasojojin kasar Somaliya,da hadin gwiwar rundunar AMISOM,sun kaddamar da hare-hare a yankin ne, a yunkurin su na karbe ikon yankin daga hannun mayakan Al shabab. Shino ya kara da cewa za a ci gaba da fafatawa har sai an cimma nasarar kwace dukkanin yankunan kudancin kasar daga ikon 'yan ta'adda.
Cikin shekaru biyun da suka gabata, gamayyar sojojin tawagar AMISOM da dakarun kasar ta Somali,sun kwace sassa da dama dake kudanci da tsakiyar kasar daga mayakan na Al-Shabab mai alaka da Al-Qaida. Sai dai kuma a daya hannun, mayakan kungiyar na ci gaba da kai hare-haren sari ka noke a lokuta daban daban a Mogadishu fadar gwamanatin kasar.