in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin bom a fadar gwamnatin Somaliya ya hallaka mutane 9
2015-09-22 11:13:07 cri
An kai harin bom da aka dasa cikin mota a fadar shugaban kasar Somaliya da ke birnin Mogadishu a jiya Litinin, lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 9, tare da jikkata wasu 14.

Wata majiya ta ce, wata mota dauke da bom ta fashe ne a daren ranar Litinin a kusa da mashigar fadar shugaban kasar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 9 ciki har da wasu sojojin gwamnati 2 kana da 'yan kasashen waje 3, tare da jikkatar wasu 14.

A wannan rana, wasu jami'an gwamnatin kasar da wakilan kasashen waje sun halarci taron a fadar shugaban kasar, dangane da babban zabe da za a gudanar a shekara mai zuwa, yayin da aka samu fasewar bom din, akasarin mahalartar taron sun watse, a cikin wadanda suka jikkata akwai wasu jami'ai 'yan kalilan da ba su tafi ba.

Kungiyar Al-shabbab ta Somaliya ta sanar da daukar alhakin kai harin (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China