Mr. Liu ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin taron kwamitin tsaron MDDr da aka gudanar don gane da halin da kasar Somalia ke ciki. Ya ce kasar Sin na fatan kasashen duniya za su rungumi akidar kyautata yanayin jagoranci a kasar ta Somaliya, bisa lura da bukatun al'ummar kasar.
Har ila yau Mr. Liu ya bayyana bukatar taimakawa gwamnatin kasar da dabarun inganta jagoranci, tare da karfafa hukumomin ta a matakai daban daban, tare kuma da bunkasa manufar sulhunta 'yan kasar.
A wani ci gaban kuma kwamitin tsaron MDD ya amince da wani kuduri, na kafa ofishi da zai rika tallafawa ayyukan MDD a kasar Somalia ko UNSOS a takaice, ofishin da kuma zai maye gurbin wanda ke tallafawa ayyukan tawagar AMISOM. Zai kuma rika taimakawa ayyukan ofishin tawagar bada tallafi ta MDD, da kuma na lura da ayyukan sojin Somaliya. (Saminu)