Rahotanni daga Bula-Burte na kasar Somaliya ya tabbatar da cewar an hallaka mayakan Al-Shabaab guda 2 sannan an kame wassu da ake zargi 'yan kungiyar ne su 7 a lokacin wani samame da sojojin kasar da hadin gwiwwar sojojin kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU a birnin dake tsakiyar kasar.
Jami'an gwamnati sun tabbatar da mutuwar 'yan kungiyar ta Al-Shabaab su 2 da kuma kame sauran magoya bayan su a garin na Bula-Burte, wanda yake yankin Hiiraan a tsakiyar Somaliya.
Abdi'asis Ibrahim Durow wani jami'in gwmanti a wajen ya shaida ma kamfanin dillancin labarai na kasar Sin na Xinhua cewa, sojojin gwamnati da goyon bayan sojin kungiyar AU sun kai samame cikin nasara don tarwatsa kayayyakin kungiyar ta Al-Shabaab.
Ya bayyana cewa an samu nasarar wargaza maboyar su, aka hallaka mutane 2 sannan aka kame wassu guda 7 maso mara masu baya, bayan da aka kwace muggan makamai a lokacin samamen.
Ya ce za'a binciki wadanda aka kama domin samun karin bayanai a kan ayyukan kungiyar ta Al-Shabaab. (Fatimah Jibril)