Kwamitin ya kuma bayyana damuwar shi matuka a yadda ake fuskantar matsanancin hali na isar da kayayyakin jin kai a Somaliya, tare da yin suka da kakkausar murya ga duk wani bangaren da ke kokarin kawo cikas a wannan aikin ko kuma almabuzzaranci da ko karkatar da kayayyakin jin kan.
Haka kuma kwamitin ya tabbatar da dokar hana shigarwa ko fitar da gawayi daga Somaliyan tare da yin maraba da kokarin sojojin hadin kai na teku wajen tarwatsa duk wani yunkurin shigar da gawayin ko fitar da shi da Somaliyan saboda cinikin gawayin yana kawo kudin ga mayakan al-shabaab.
A game da Eritrea kuwa, shawarar da kwamitin ya cimmawa yayi maraba da kokarin kungiyar sa ido ta Somaliya da Eritrea wato SEMG na hada kai da gwamnatin Eritrea tare da jaddada fatan cewa gwamnatin Eritrea zai kokarta na ganin an shigar da kungiyar a cikin kasar domin ta samu aiwatar da aikinta yadda ya kamata.