Wani babban jami'in soja a yankin na Gedo mai suna Isma'il Abdi wanda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin aukuwar harin na ranar Laraba,ya kuma ce an jikkata mayakan Al-Shabaab 30,tare da lalata sansanoninsu baya ga makaman mayakan da aka kwace.
Sai dai jami'in ya ce, sun yi asarar sojoji guda 9, da kuma manyan jami'an gwamnati guda biyu.
Yanzu dai kauyen yana hannun ikon dakarun gwamnati ne, bayan da suka fatattaki mayakan na Al-Shabaab daga cikinsa.(Ibrahim)